Mai shigar da kara na kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa (ICC), Karim Khan, ya yi watsi da bukatar Isra’ila na yin watsi da sammacin kama Firaminista Benjamin Netanyahu da tsohon ministan tsaro Yoav Gallant kan laifukan yaki da suka aikata a Gaza.
Mai gabatar da kara na kotun ya bayyana cewa karar a halin yanzu ba ta da wani tasiri amma ana iya magance ta a matakan shari’a na gaba.
Majiyoyin Isra’ila sun bayyana cewa a ranar Laraba gwamnatin Isra’ila ta mika wasu takardu biyu ga kotun daukaka kara ta ICC, wadanda ke adawa da sammacin kama jami’an kasar.
A cikin daftarin farko mai shafi 14 da aka mika, Isra’ila ta kalubalanci ikon kotun hukunta manyan laifuka ta ICC na gudanar da shari’ar tare da bayar da sammaci kan Netanyahu da Gallant.
Takardar ta biyu mai dauke da shafuka 13 tana nuna rashin amincewa da matakin kotun ta ICC.
A cewar kafar yada labaran Isra’ila Ynet, Isra’ila ta bukaci a dakatar da sammacin, tare da bayyana fatan kotun ta ICC za ta sake duba matsayinta.
A ranar Alhamis 21 ga watan Nuwamba, kotun ta ICC ta bayar da sammacin kamo Netanyahu da Gallant bisa zargin laifukan yaki, cin zarafin bil’adama, da kuma amfani da yunwa a matsayin makami kan fararen hula a Gaza.