Search
Close this search box.

IAEA, Ta Bukaci Ci Gaba Da Tattaunawa Da Iran A Matakin Koli

Shugaban Hukumar kula da Makamashin Nukiliya Ta Duniya, Rafael Grossi, ya bukaci ci gaba da tattaunawa da mahukuntan Iran a matakin koli, game da batutuwan

Shugaban Hukumar kula da Makamashin Nukiliya Ta Duniya, Rafael Grossi, ya bukaci ci gaba da tattaunawa da mahukuntan Iran a matakin koli, game da batutuwan da ake takaddama akansu.

Mista Grossi ya tabo batun ziyarar da ya kai birnin Tehran a baya-bayan nan da kuma yarjejeniyar da aka cimma da jami’an Jamhuriyar Musulunci ta Iran kan ci gaba da aiwatar da sanarwar da aka fitar a ranar 4 ga Maris da nufin warware dukkan wasu batutuwan da suka sa a gaba, inda ya yi kira da a ci gaba da gudanar da shawarwarin don ci gaba da yin mu’amala da tattaunawa a tsakaninsu a matakin koli tare da sabuwar gwamnatin Iran.

Da yake magana a wajen bude taron hukumar gudanarwar hukumar ta IAEA yau Litinin, Rafael Grossi ya ce: “Ina maraba da yadda Iran ta amince da cewa sanarwar hadin gwiwa ta ranar 4 ga Maris tana ci gaba da samar da tsarin hadin gwiwa da hukumar ta IAEA da kuma tinkarar batutuwan da suka dace.

Ya kuma bukaci sabuwar gwamnatin Iran da ta ci gaba da tattaunawa bayan ziyarar da ya kai Iran a kwanakin baya da kuma ganawarsa da ministan harkokin wajen kasar Hossein Amir Abdollahian da Ali Bagheri Kani.

Yau Litinin ne aka fara taron shugabannin hukumar IAEA tare da halartar kasashe mambobin hukumar 35 a Vienna.

Za a ci gaba da taron har zuwa ranar Juma’a, kuma mahalarta za su tattauna batutuwa daban-daban, ciki har da aiwatar da yarjejeniyar tsaro da karfafa ayyukan kimiyya da bincike na hukumar ta IAEA.

Iran za ta kasance cikin ajandar wannan taro kuma za’a tattauna ayyukan nukiliyar kasar bisa tsarin kuduri mai lamba 2231 na kwamitin sulhu na MDD.

Share

5 1 vote
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments