Babban daraktan hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA ya bayyana fatansa na ganin an farfado da yarjejeniyar nukuliyar Iran.
Rafael Grossi, ya yi wanan tsokacin ne a matsayin amsa ga bukatar sabon shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian, wanda son a sabunta tattaunawa da nufin samun fahimtar juna game da shirin nukiliyar Iran na zaman lafiya.
Ya bayyana fatan cewa za a farfado da yarjejeniyar nukiliyar Iran, da nufin tabbatar da zaman lafiya na ayyukan nukiliyar Iran.
Rafael Grossi, a wata hira da ya yi da tashar Al-Arabiya, ya ambaci shirin nukiliyar Iran na zaman lafiya, ya kuma bayyana damuwarsa kan yadda kasar ke ci gaba da tara sinadarin uranium da ta inganta.