Hurmuz: Katafaren Jiran Contenoni Ya Nutse A Hurmuz

Wani babban katafaren jirgin daukar kaya, dauke da kwantenoni kimani 2500 ya fada kan nakiya a cikin mashigar ruwa ta Hurmuz a jiya Talata kuma

Wani babban katafaren jirgin daukar kaya, dauke da kwantenoni kimani 2500 ya fada kan nakiya a cikin mashigar ruwa ta Hurmuz a jiya Talata kuma hakan yayi sanadiyyar nutsewarsa a cikin ruwa.

Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ya nakalto majiyar IRGC na tabbatar da wannan labarin ta kuma kara da cewa, jirgin ruwan dauke da kwantenoni kimani 2500 ya fada kan nakiya a lokacinda yake kokarin wucewa ta barauniyar hanya a mashigar ruwan.

Jami’i mai magana da yawan IRGC NAVY ya fadawa Presstv kan cewa, jirgin ya sabawa dokokin da hukuma mai kula da mashigar ruwa ta Hurmuz ta kasar Iran ta shimfida don haka ya fada kan nakiya wanda ya fashe ya kuma sa jirgin ya kama da wuta ya kuma nutse a cikin ruwa a yammacin jiya Laraba.

Majiyar ta kara da cewa, IRGC ta sha nanata gargadi kan cewa ba wanda zai iya wucewa ta mashigar ko ya fita sai da izinin hukumar. Amma da dama suna yaudaruwa da maganganun yan siyasar Amurka musamman shugaban kasar wanda ya sha nanata cewa, mashigar a bude take.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted