Human Rights Watch Ta Zargi Isra’ila Da Aikata Kisan Kiyashi” A Gaza

Kungiyar kare hakkin bil adama ta kasa da kasa Human Rights Watch ta fitar da wani rahoto wanda a cikinsa ta yi imanin cewa, Isra’ila

Kungiyar kare hakkin bil adama ta kasa da kasa Human Rights Watch ta fitar da wani rahoto wanda a cikinsa ta yi imanin cewa, Isra’ila na aikata “ayyukan kisan kiyashi” ta hanyar takaita “hanyar samar da ruwan sha” ga Falasdinawa a Gaza.

Rahoton ya ce “Hukumomin Isra’ila sun kirkiro da gangan da duk wasu hanyoyi na hana fararen hula Falasdinawa a yankin samun isasshen ruwa.

Kungiyar ta kara da cewa, Isra’ila ce ke da alhakin aikata laifin cin zarafin bil’adama da kuma ayyukan kisan kare dangi a Gaza.”

Tun farkon yakin da ta shelanta da kungiyar Hamas, Isra’ila ta tashe duk wasu hanyoyin samar da ababeb more rayuwa ga milyoyin al’ummar Gaza.

Tun a ranar 7 ga watan Oktoban shekarar 2023 ne dakarun Isra’ila suka fara kai hare-hare a zirin Gaza tare da goyan Amurka, wanda ya zuwa yanzu ya lakume rayukan Falasdinawa sama da dubu 45, galibinsu mata da kananan yara.

Isra’ila dai ta yi biris da duk kiraye-kirayen da kasashe da kungiyoyin kasa da kasa ke yi mata na ta dakatar da yakin da ta ke a Gaza.

Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ta fitar da sammacin kame mata firaministan Isra’ilar Benjamin Netanyahu da tsohon ministan yakinsa Yeav Gallant, bisa zargin aikata laifukan yaki a Gaza saidai Isra’ilar da Amurka sun yi fatali da matakin kotun da suka dangnata da abin kunya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments