Hukumar tarayyar turai ta gabatar da shawara ga kasashe mambobi da su jingine aiki da yarjejeniyar da aka kulla ta kasuwanci da HKI saboda yakin Gaza.
A yau Laraba ne dai hukumar tarayyar turai din ta bijiro da wannan shawarar ga kasashen mambobi,sai dai kuma babu cikakken goyon baya daga mafi yawancin kasashen kungiyar da zai sa a yi aiki da shi.
Ita kuwa jami’ar harkokin wajen ta tarayyar turai din Kaya Kalas ta gabatar da shawarar a kakaba takunkumi akan wasu ministoci biyu na HKI da kuma ‘yan share wuri zauna da suke amfani da karfi akan Falasdinawa.
Da akwai kungiyoyin kare hakkin bil’adama guda 84 da suke yin kira a yanke duk wata alaka ta kasuwanci da zuba hannun jari da HKI,daga cikinsu har da “Amnesty International”.
Kungiyoyin dai suna son ganin kasashen na turai da su ka hada tarayyar turai, kasar Birtaniya sun dauki matakai masu kwari na yanke alakar tattalin arziki da HKI.