Hukumar makamashi ta duniya ta sanar da cewa; duniya za ta ci gaba da fuskantar karancin makamashin “Diezel” daga nan har zuwa 2027.
Hukumar ya bayyana cewa koma bayan da aka samu na tace danyan man fetur da kuma Diezel suna da alaka ne da yakin da aka shelanta akan Iran.
Bugu da kari ta ce a halin yanzu da akwai matsi mai yawa akan kasuwar neman wannan makamashin saboda kwan-gaba-kwan baya da ake samu a kasuwar gabatar da shi.
Sai dai kuma hukumar ta yi hasashen cewa zuwa karshen wannan shekarar aikin matatun mai zai karu, kuma za a fara adana mai, amma duk da hakan, za a iya cike gurbin makamashin da aka rasa ba a cikin shekara daya.
Kasashe mambobi a cikin wannan hukumar sun amince da fitar da ganga miliyan daya na man fetur da kuma Diezel, domin rage hauhawar farashi akasuwanni.
An dauki wannan matakin ne dai a lokacin da tattalin arzikin duniya yake fuskantar matsin lamba. Ana amfani ne da makamahsin Diezel ne dai a cikin manyan masana’antu da aikin gona da kuma sufurin manyan motoci.
Hukumar ta kuma bayyana cewa; An sami raguwar fitar makamashin Diezel daga gabas ta tsakiya da kuma Rasha da adadin da ya kai miliyan da 300,000 a kowace rana.