Hukumar Kwallon Kafa Ta Falasdinu Ta Bukaci Fifa Ta Dakatar Da Isra’ila

Hukumar kwallon kafa ta Falasdinu ta bukaci, a dakatar da Isra’ila “nan take” daga hukumar kula da kwallon kafa ta duniya Fifa, kamar yadda Shugaban

Hukumar kwallon kafa ta Falasdinu ta bukaci, a dakatar da Isra’ila “nan take” daga hukumar kula da kwallon kafa ta duniya Fifa, kamar yadda Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Falasdinu Jibril Rajoub, ya bayyanawa takwaransa na Fifa Gianni Infantino a lokacin taron fifa a Bangkok, in ji AFP.

A cewar Rajoub, Falasdinu za ta yi aiki don ci gaba da yada wasannin motsa jiki a dukkan yankunan kasar Falasdinu da Majalisar Dinkin Duniya ta amince da su, da suka hada da gabar yamma da kogin Jordan, Gabashin Kudus da zirin Gaza, bisa doka da ka’idojin FIFA.

M. Rajoub, ya bukaci da a dorawa hukumar kwallon kafa ta Isra’ila alhakin keta dokokin FIFA, wanda dole ne ya shafi ayyukan hukumar kwallon kafa ta Isra’ila.

Rajoub ya ce: “Mun gano cewa hukumar FA ta Isra’ila ta aikata laifuka da dama da suka saba wa dokokin FIFA, ciki har da shirya gasa a yankunan Falasdinu.

Ya kara da cewa, daga cikin irin wannan cin zarafi har da bayyanar nuna wariyar launin fata, wadanda muke ganin sun bayyana a cikin ayyukan sojojin mamaya, wanda ya tilasta mana dakatar da duk wasu harkokin wasanni a duk yankunan Falasdinu. Yammacin Kogin Jordan, Gabashin Kudus da Zirin Gaza.

A nasu bangaren, sojojin Isra’ila sun ce: “An tilasta mana dakatar da duk wasu harkokin wasanni, kuma ba mu iya shirya gasar ko ma karbar bakuncin kungiyoyin kasa a kasarmu a wasannin nahiyoyi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments