Hukumar FIFA Na Shirin Samar Da Karin Fam Biliyan 2.6

hukumar kwallon kafa ta duniya fifa na shirin kara habaka harkar kwallon kafa a duniya inda zata samar da kudi masu yawa

Hukumar FIFA za ta ware karin fam biliyan 2 da miliyan 600, kwatankwacin dala biliyan 3 da miliyan 400 don habaka wasan kwallon kafa a faɗin duniya tsakanin shekarun 2027 zuwa 2030.

Shugaban FIFA, Gianni Infantino, zai gabatar da wannan shawarar ga Majalisar FIFA bayan hukumar ta samu dimbin riba daga gasar cin Kofin Duniya ta shekarar 2026.

Wannan sabon tsari ya fito ne bayan da manyan hukumomin kwallon kafa kamar UEFA da CONCACAF suka nuna  adawa ga tsohon shirin Infantino na sayar da hannun jarin gasar FIFA ga masu saka jari na kashin kansu.

Wannan karin kudi ya kawo jimillar kudaden da za a kashe wajen habaka wasan zuwa fam biliyan 4 da ɗigo 83 kwatankwacin dala biliyan 6.35, inda aka fi mayar da hankali kan kwallon kafar mata da na matasa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted