Hukumar Falasdinu Ta Dakatar Da Ayyukan Gidan Talabijin Na Al’ Jazeera

Hukumar Falasdinawa ta dakatar da aikin gidan talabijin na Al Jazeera na wani dan lokaci a yankin Yammacin Kogin Jordan bisa zargin tunzura jama’a,” in

Hukumar Falasdinawa ta dakatar da aikin gidan talabijin na Al Jazeera na wani dan lokaci a yankin Yammacin Kogin Jordan bisa zargin tunzura jama’a,” in ji kamfanin dillancin labaran Falasdinu Wafa.

Wani kwamitin ministoci da ya hada da ma’aikatar al’adu, cikin gida da na sadarwa ne ya yanke shawarar dakatar da ayyukan gidan Al’Jazeera saboda abin da suka bayyana a matsayin yada labaren tunzura jama’a da rahotanni masu cike da yaudara da tayar da hankali” a yankin, in ji Wafa a ranar Laraba.

Babu dai wani martani daga kafar yada labarai ta Aljazeera.

Matakin dai na zuwa ne bayan da kungiyar Fatah a Falasdinu ta haramtawa tashar Al Jazeera rahoto daga gundumar Jenin da ke arewacin gabar yammacin kogin Jordan, saboda kawo labarin fada tsakanin jami’an tsaron Falasdinu da kungiyoyin Falasdinu masu dauke da makamai a yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments