Hukumar ( EFCC) Ta Najeriya Ta Kame  Kusan Mutane 800 Masu Damfara Ta Hanyar Intanet

Hkumar da take fada da cin hanci da rasahawa da kuma yi wa tattalin arzikin kasar almundahana ta ( EFCC) ta kama mutane 792 wadanda

Hkumar da take fada da cin hanci da rasahawa da kuma yi wa tattalin arzikin kasar almundahana ta ( EFCC) ta kama mutane 792 wadanda suke damfarar mutane ta hanyar sadarwa ta yanar gizo.

Hukumar ta ce mutanen da aka kama sun hada ‘yan kasar China 148 da ‘yan Filipine 40, a wani gini mai hawa 10 a birnin Ikko.

Kakakin Hukumar ta EFCC Wilson Uwujaren ya ce; Ginin da aka kama mutanen ana amfani da shi ne da sunan; Wurin yin kira na tarho,amma kuma ana damfarar Amurkawa ne da ‘yan kasashen turai. ‘Yan damfarar suna amfani da hanyoyin sadarwa na al’umma irin su WhatsApp da Instagram. Haka nan kuma suna Magana da wadanda suke son damfara da sunan soyayya ko kuma wata dama ta zuba hannun hari,musamman kudaden nan na Crypto.

Hukumar ta EFCC ta kwace na’urori masu kwakwalwa, wayoyin hannu da motoci, kuma suna aiki da abokinsu na kasashen waje domin gudanar da bincike.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments