Kamfanin dillancin labarun “Irna” na Iran ya nakalto hukumar agaji ta “UNRWA” tana cewa, HKI tana cigaba da hana a shigar da kayan agaji zuwa zirin Gaza
Sanarwar ta kuma ce, HKI ta hanawa ma’aikatan hukumar ta “UNRWA” kai wa mazauna Arewacin Gaza, kayan agaji.
Phillip Lazariani wana shi ne babban jami’in hukumar Agajin ta UNRWA, ya ce; Da akwai bukatar HKI ta sauya siyasarta ta hana kai kayan agaji, da kashe masu aikin ceto da kuma kai wa Asibitoci hare-hare.”
Daga fara yaki akan Gaza zuwa yanzu, sojojin HKI sun kashe ma’aikatan hukumar agajin ta “UNRWA” su 176.
Phillip Lazariani ya kuma yi gargadi akan mummunan halin da za a iya shiga a cikin yankin na Gaza, musamman a fuskokin asibitoci da sauran cibiyoyin kiwon lafiya, don haka ya bukaci a kawo karshen yakin nan cikin gaggawa.