Isra’ila Ta Kai Hari Da Makamai Mazu Linzami A  Wasu Yankuna Na Yamen

Kasar yamen itace kasar larabawa daya tilo a kasashen musulmi ta duniya da ta mike ta kalubalanci yakin kare dangi da Haramtacciyar Kasar Isra’ila take

Kasar yamen itace kasar larabawa daya tilo a kasashen musulmi ta duniya da ta mike ta kalubalanci yakin kare dangi da Haramtacciyar Kasar Isra’ila take ci gaba da yi kan yankin falasdinu, da Israila ta kira da yunkurin samar da fadaddiyar Isra’ila.

Wani babban jami’in soji na kasar yaman ya fadi cewa za su ladabatar da isra’ila kan wannan hari da ta kai, Isra’ila ta kai hari kan wuraren farar hula, inda mutane da dama suka yi shahada wasu kuma suka jikkata, kuma duk wannan sadaukarwa ba zai hana ci gaba da goyon bayan alummr gaza ba, da kuma ladabtar da Isra’ila.

Wasu majiyar labarai ciki har da kamfanin dillancin labarai na reuters da ma tashar talabijin din isra’ila sun sanar cewa isra’ila ta kai hari kan ma’aikatar tsaro kasar yamen ne, sai dai gwamnatin yamen ta musanta hakan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments