Kafafen watsa labarun HKI sun sanar da cewa, adadin sojojinsu da su ka jikkata sun kai 20, da aka kai wasu daga cikinsu asibitin dake garin Safad.
Da safiyar yau Alhamis majiyar sojojin mamayar na HKI ta sanar da cewa daya daga cikin sojojinta ya halaka a fadan da suke yi da mayakan Hizbullah a kudancin Lebanon.
Bugu da kari majiyar ta ce, daga lokacin da sojojin HKI suka fara kokarin yin kutse ta kasa cikin kudancin Lebanon an kashe 12 daga cikinsu, sai dai majiyar Hizbullah ta tabbatar da cewa adadain wadanda su ka kashe din sun haura 35 da kuma jikkata wasu 200.