HKI Ta Kashe Wani Babban A Cikin Shuwagabannin Falasdinawa

Daya daga cikin shuwagabannin Falasdinawa ya yi shahada sanadiyyar hare-haren da sojojin HKI suka kai kan zirin gaza. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran

Daya daga cikin shuwagabannin Falasdinawa ya yi shahada sanadiyyar hare-haren da sojojin HKI suka kai kan zirin gaza.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ya bayyana cewa Asa’d Abu Sharia shi ne baban sakataren kungiyar ‘Dakarun Palastinewa”. Wacce aka kafa a shekara ta 2001 M.

Kungiyar kanta ta tabbatar da wannan labarin ta kuma bayyana cewa ya dade yana shugabantar wannan kungiyar sannan a ranar 7 ga watan Octoban shekara ta 2023 ya shiga cikin yakin da aka fara kan HKI kuma dakarunsa sun kama yahudawa da dama suka shigo da su su gaza. Banda haka shi ne yake jagorantar bangaren soje na kungiyarsa. Sau da dama ya jagoranci Falasdinawa a yaki da yahudawan a Gaza. Sannan kungiyar tana da reshe a yankin yamma da kogin Jordan.

A wani labarin kuma kungiyar ta kara da cewa tare da shi akwai dan uwansa Ahmed Abu Sharia, ko wanda akewa  Lakabi da  Abu Falasteen, sun yi shahada tare. Banda haka kafin shahadarsa Abu Sharia ya rasa danginsa na kusa kimani 150 a yankin tufanul Aksa ya zuwa yanzu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments