Majiyar sojojin kasar Lebanon ta bata labarin cewa jiragen yakin HKI sun kai hare-hare kan wasu wurare a kudancin kasar Lebanon inda suka yi sanadiyyar mutuwar mutum guda a jiya Jumma’a da kuma wani mutum guda a ranar Alhamis.
Tashar talabijan ta Al-Manar ta tabbatar da wadan nan hare-hare da kuma asarar rayuka da aka yi a garin Al-mansouri a lardun Tyre a jiya jumma’a da kuma Maifadoun a ranar Alhamis.
Labarin ya kara da cewa HKI tana ci gaba da kai hare-hare da kuma kashe mutanen kudancin kasar Lebanon tun bayan tsagaita wuta da aka cimma da su a karshen shekara ta 2024.
A daren Alhamis jirgin HKI na yaki kuma wanda ake sarrafashi daga nesa ya kai hari kan garin Maifadoun da ke kusa da Nabadiyya a lardin Tyre. Kuma ya kashe wani da ake kira Walid Olleik, dan taxi wanda yake taimaka sojojin kasar Lebanon sosai a duk abinda zai iya a yankin. A wani lokacin yakan daukesu kyauta ya kaisu inda suke bukata.
HKI dai ta ce gaba da keta hurumin yarjeniya mai lamba 1701 ta shekara ta 2006 daga asali sannan aka sabontata a ranar 27 ga watan Nuwamban shekara ta 2024.
Tun lokacin ya zuwa yanzu gwamnatin HKI ta keta wannan yarjeniyar har fiye da dubu guda, kuma sun kashe mutanen kudancin kasar Lebanon har 435.