Gamayyar Jiragen ruwan ceto ko (FFC) ta bada sanarwan cewa sojojin HKI a yau Laraba sun kai faramaki kan wasu jiragen gamayyar a tazarar kilomitan ruwa 120nm kacal daga zirin Gaza.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar FFC tana cewa hotunan bidiyo da na tsaye, duk sun nuna lokacinda sojojin yahudawan suka farwa jiragen na ceton Gaza.
Labarin ya kara da cewa sojojin yahudawan sun dakatar da wasu jiragen a ruwayen kasa da kasa, wanda bata da hakkin yin hakan. Jiragen ruwan ceton dai suna dauke da kayakin agaji wadanda suka kai dalar Amurka $110,000, kama hada da kayakin aikin likita da magunguna da wasu kayakin asbiti.
Labarin ya nakalto kafafen yada labaran yahudawan na cewa sun karkatar da wasu jiragen ruwan zuwa tshar jiragen ruwa ta Ashdod, inda ake saran gwamnatin yahudawan zata tilasta masu ficewa daga kasar Falasdinu da aka mamaye.
Jiragen ruwan ceton dai a wannan karon sun kai kimani 40 dauke da mutane kimani 500. Kuma wadanda HKI ta tsaresu a gidajen yarin kasar a makon da ya gabata sun bayyana cewa an azabtar da su, a inda aka tsaresu. Har yanzun kuma yahudawan na tsare da mutane 6 daga cikinsu.