Rahotannin da suke fitowa daga kasar Syria sun ce da safiyar yau Alhamis HKI ta kai hare-hare a kan Birged-birged na sojojin Syria na 107 da 132 a yankin Lazikiyya a arewacin kasar.
Dama dai a jiya HKI ta kai hare-haren masu tsanani a birnin Damascuss akan ginin ma’aikatar tsaro, babbar shalkwatar sojoji da kuma kusa da fadar shugaban kasa.
Sojojin HKI sun sanar da cewa sun kai hare-haren ne akan cibiyoyin soja da daya cikinsu yana kusa da fadar shugaban kasa.
Wasu yankunan da HKI ta kai wa hare-haren, sun hada da garin Dar’a a kudancin kasar, da kuma babban hanyar dake kusa shi, sai kuma Suwaidaa.