Search
Close this search box.

HKI Ta Ce, sojojinta 21 Ne Su Ka Halaka  Daga Watan Satumba Zuwa Yanzu

A wata sanarwa da sojojin mamayar su ka fitar sun bayyana cewa:  An kasha wasu sojoji biyu a tsakiyar Gaza, sai kuma wani soja guda

A wata sanarwa da sojojin mamayar su ka fitar sun bayyana cewa:  An kasha wasu sojoji biyu a tsakiyar Gaza, sai kuma wani soja guda daya a Rafah, yayinda da aka kashe wasu 8  a cikin motar daukar sojoji shi ma a Rafah.

Bugu da kari sanarwar ta ce a raanr 15 ga watan nan na Yuni an kashe wasu sojojin biyu, yayin da wani guda kuma ya halaka a ranar 10 ga watan na Yuni.

Har ila yau sanarwar ta ‘yan mamayar ta ce, an kashe wasu sojojin 4 a wani kwanton bauna da aka yi musu a tsakiyar Rafah.

A yankin sansanin Nusairat kuwa an kashe wani babban jami’in sojan mamaya guda daya, a lokacin kokarin kwato  fursunonin da ‘yan gwagwarmaya suke rike da su.

Daga kasar Lebanon ma kungiyar Hizbullah ta kai wani harin da jirgin sama maras matuki wanda ya yi sanadin  kashe sojan mamaya guda.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments