Ministan yaki na HKI Israel Katz ya sanar da cewa; gwamantinsa ce take da alhakin yi wa Isma’ila Haniyya tsohon shugaban kungiyar Hamas kisan gilla a cikin birnin Tehran.
A jiya Litinin ne dai Katz ya bayyana hakan inda ya ce; Za mu kai wa ‘yan Husi hari mai tsanani, mu kashe shugabanninsu, kamar yadda mu ka yi wa Haniyya, Yahya Sinwar da Nasralalh, a cikin biranen Tehran, Gaza da kuma Lebanon. Wannan shi ne abinda za mu yi a Hudaida da Sanaa.”
Ministan yakin na HKI ya kuma ce; Duk wanda ya dagawa Isra’ila yatsa, to za mu gutsure wannan hannun.”
Bugu da kari Katz ya bayyana cewa, makomar Sanaa da Hudaida za ta zama irin ta Gaza da Lebanon.
Wannan dai shi ne karon farko da HKI ta yi furuci da cewa ita ce ta kashe Shahid Isma’ila Haniyyah a cikin birnin Tehran.
A ranar 31 ga watan Yuli na wannan shekara mai karewa ne dai Isra’ilan ta yi wa Isma’ila Haniyya kisan gilla anan birnin Tehran, a daidai lokacin da ake batun tsagaita wutar yaki.
Haniyya dai ya zo Tehran a lokacin domin halartar bikin rantsar da sabon shugaban kasar Iran Mas’ud Fizishkiyan, inda kwana daya bayan hakan ‘yan sahayoniyar su ka yi masa kisan gilla.
Shi kuwa Sayyid Hassan Nasrallah, an yi masa kisan gilla ne a ranar 27 ga watan Satumba a birnin Beirut, sai kuma Yahya Sinwar a ranar 16 ga watan Oktoba a Gaza.