Kakakin sojojin HKI ya bada sanarwan cewa sojojin kasar sun kashe sabon shugaban kungiyar Hamas Yahya Sinwar a wata fafatawa da suka shiga da shi da wasu manya manyan jami’an kungiyar a garin Rafah da ke kan iyakar kasar Masar da kuma zirin Gaza a jiya Alhamis.
Kungiyar Hamas dai bata tabbatar da wannan labarin ba. Amma gwamnatin Amurka kuma ta ce bata da hannu a kissan Yahyah Sinwar .
Shugaban kungiyar ta Hamas ya gaji marigayi Isma’il Haniyya ne bayan da HKI ta kashe shi a birnin Tehran a ranar 31 ga watan Yulin da ya gabata a lokacinda yake halattar bukukuwan rantsar da sabon shugaban kasar Iran Masoud Pezeskiyan a birnin Tehran.
Sinwar dai ya sha dauri a hanun yahudawan har na tsawon shekaru fiye da 20, amma kuma yahudawan suna ganin shi ne shugaba da kuma wanda ya kawo dabarar yakin tufanul Aksa wanda kungiyar ta fara a ranar 7 ga watan Octoban shekara ta 2023.
Ya zuwa yanzu yahudawan sun kashe Falasdinawa akalla dubu 42 a gaza kadai a ya yin da wasu kimani dubu 97 suka ji raunin. mafiyansu mata da yara.
A wani labarin kuma wasu majiyoyin gwamnatin Amurka sun ce Amurka ta bukaci HKI ta janye daga gaza ta kuma bude kofofin shiga yankin don shigo da kayakin agaji. Sai masana suna ganin gwamnatin Biden ta bayyana hake kawai don neman kuri’u a zaben a watan Nuwamba mai zuwa a kasar Amurka, bata nufin abinda take fada.