Sojojin HKI suna cigaba da kai wa kauyuka da garuruwan dake kudancin Lebanon hare-hare ta hanyar amfani da nau’oin makamai.
Daga cikin garuruwan da sojojin HKI su ka kai wa hari a jiya Laraba da a kwai “Ramiyah”, Aynat da Balida.
A gefe daya kungiyar ta Hizbullah ta kai wa sansanoni da cibiyoyin ‘yan mamaya hare-hare. Yankunan hare-haren na Hizbullah sun kunshi Zariat, Nadhua’, Fadudha, Shomirah, da Shatula.
Tun a ranar 8 ga watan Oktoba ne, wato kwana daya bayan farmakin “Guguwar Aqsa’ dakarun kungiyar Hizbullah su ka bude kai wa sojojin mamayar HKI hare-hare da zummar taya Falasdinawan Gaza fada.
Bayanan da kungiyar take fitarwa a kusan kullum dangane da hare-hare suna bayyana cewa ana kai su ne saboda goyon bayan Falasdinawa.