HKI: Har Yanzu Hizbullah Tana Nan Da karfinta

Kafafen watsa labarun HKI sun ambaci cewa, har yanzu Hizbullah tana nan da karfinta, kuma gwamatin Lebanon ba za ta iya raba ta da makaman

Kafafen watsa labarun HKI sun ambaci cewa, har yanzu Hizbullah tana nan da karfinta, kuma gwamatin Lebanon ba za ta iya raba ta da makaman da take da sub a.

Tashar talabijin din “Isra’il News 24” ta ambato wani dan sahayoniya Barukh Yadid yana cewa; Dan sakon Amurka Thomas Barak ya isa Lebanon a karo na uku a cikin wata daya da rabi yana dauke da sako daya daga Amurka da shi ne kwace makaman Hizbullah.

Haka nan kuma ya ce; Abinda ya kawo Barak zuwa Lebanon a wannan lokacin shi ne karbar jawabi daga gwamantin Lebanon akan wannan batun na kwance damarar Hizbullah.”

Dan sakon na Amurka ya isa Lebanon bayan wucewar watanni 7 daga jawabin shugaban kasar Joseph Aun na cewa; Gwamnati ce kadai za ta zama mai rike da makamai.

Har ila yau ya ce,  Amurka tana sane da cewa, gwamnatin Lebanon ba za ta iya kwace makaman Lebanon ba.

Wani sashe na jawabin nashi ya kunshi cewa; Gwiwa ta yi sanyi a Tel Aviv cewa, Shirin sake Shata gabas ta tsakiya zai yiyu, domin dukkanin hare-haren da Isra’ila take kai wa Lebanon da Syria ba zai kai ga samar da sabuwar gabas ta tsakiya ba.

Tun bayan tsagaita wutar yaki a tsakanin Lebanon da HKI, Amurka take kokarin ganin shugabannin kasar ta Lebanon sun raba Hizbullah da makamanta.

Ita dai kungiyar ta Hizbullah ta sha nanta cewa ba za ta kwance damarar yaki da HKI, amma a shirye take ta bude tattaunawa da mahkuntan Lebanon akan yadda za bullo da sabuwar dabarar tsaro wacce za ta ba da damar a ci gaba da riko da gwagwarmaya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments