Hizbullah Ta Kashe Sojojin Mamayar HKI Da Dama A Kudancin Kasar

Dakarun kungiyar Hizbullah wacce ta yi taho mu gama da sojojin mamayar HKI a kusa da garin Kauzah, inda aka yi amfani da makamai mabanbanta

Dakarun kungiyar Hizbullah wacce ta yi taho mu gama da sojojin mamayar HKI a kusa da garin Kauzah, inda aka yi amfani da makamai mabanbanta da hakan ya yi sanadiyyar kashe da dama daga cikinsu da kuma jikkata wasu.

Rahotannin da suke fitowa daga filin dagar sun ambaci cewa, an ga jiragen sama masu saukar angulu 10 suna shawagi a samaniyar yankin domin daukar gawawwaki da kuma wadanda su ka jikkata.

A can cikin HKI kuwa, an ga jiragen sama masu saukar angulu suna sauka a asibitoci dauke da sojojin da su ka dauko daga filin yaki na kudancin Lebanon.

Kafafen watsa labarun HKI sun ce jirage 8 ne su ka sauka a asibitin “Rambam” dake Haifa, kadai sai kuma asibitocin “Bilinson’ da Tel Hashomir”.

Sai dai kuma sojoji sun hana fito da bayanai akan hakikanin abinda ya faru.

A wasu rahotannin da suke fitowa daga HKI da safiyar yau Alhamis sun ambaci cewa, an ji jiniyar gargadi tana kadawa a cikin garuruwa da birane 60, saboda hare-hare daga Lebanon.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments