Wani dan majalisar dokokin kasar Lebanon daga bangaren siyasa na Hizbullah ya ce kungiyar ta shirya tsaf don fuskantar kowane irin yanayi.
Mohammad Raad, ya bayyana hakan ne a wata hira da tashar talabijin al-Alam ta Iran.
Da yake watsi da barazanar da gwamnatin Sahayoniya ta yi na daukar matakin soji a kan kasar Labanon, ya jaddada cewa irin wannan tsoratarwa na da nufin inganta kwarin gwiwar sojojin Isra’ila ne a lokacin yakin Gaza.
“Gwamnatin yahudawan sahyoniya ta san cewa wadannan barazanar na kan abin izgili ne a tsakanin jam’iyyun da ke da masaniya game da rauninta].
Ya kara da cewa, kungiyar Hizbullah ta tsaya tsayin daka kan goyon bayanta ga Falasdinawa a daidai lokacin da ake ci gaba da kai munanan hare-haren soji kan zirin Gaza.
Shi dai Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu a ranar Laraba ya aika da gargadi mai tsauri ga kungiyar Hezbollah ta Lebanon, inda ya jaddada cewa sojojin Isra’ila sun shirya daukar “mataki mai karfi” kan Lebanon.
Netanyahu ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya fitar a lokacin wata ziyara da ya kai arewacin Kiryat Shmona da Isra’ila ta mamaye wanda dakarun Hezbollah suka kai wa hare-hare.