Mataimakin babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sheikh Naeem Kasim ya bayyana cewa kungiyarsa a shirye take ta fadada yakin da take fafatawa da HKI gwagwadon fadada shi da HKI ta yi, ya kuma kara da cewa kungiyarsa a shirye take ta fadada yaki da HKI zuwa matsayi mafi muni a yakin.
Sheikh Qasim ya bayyana haka ne a hirar da ta hada shi da tashar radiyo ta kamfanin dillancin labaran Sputnik na kasar Rasha a birnin Beirut babban birnin kasar Lebanon a ranar Jumma’an da ta gabata
Sheikhin malamin ya kuma kara da cewa ‘gwamnatin HKI bata da zabi in banda amincewa da bukatun kungiyar HAMAS na tsagaita bude wuta, don ba zata dakatar da budewa juna wata ba sai in an tsaida kissan fararen hula a gaza.’
Shiekh Qaseem ya kammala da cewa a halin yanzu falasdinawa da sojojin HKI suka kashe ko raunatasu a gaza sun kai tsakanin dubu 130 zuwa dubu 140, sannan ga da yunwa da karancin magunguna wadanda sauran falasdinawa suke fama da su a Gaza.. Wadannan al-amura gaba daya suna faruwa ne tare da tallafin gwamnatocin kasshen yamma wadanda suka hada da Amurka da wasu kasashen Turai, inji malamin.