Dan Majalisar mai wakiltar Hizbullah Ali Fayyadh ya yi rangadi tare da ‘yan jarida na cikin gida da kuma waje a kudancin Lebanon domin ganin girman barnar da Isra’ila ta yi a yankin. Sun ziyarci garin al-shihabiyyah da kasuwar garin da kuma garin Kharbatul-Salam har zuwa garin al-Sawanah, da ya halarci jana’izar shahidan Hizbullah.
Dan majalisar Ali Fayyadh ya yi maraba da ‘yan jaridar na gida da waje,tare jinjina musu akan yadda su ka rika daukar labarun yadda yaki ya rika tafiya da kuma halin da ake ciki bayan yaki.
Har ila yau, Ali Fayyadh ya yi ishara da martanin da Hizbullah ta mayar akan keta tsagaita wutar yaki da HKI take yi, yana mai kara da cewa abinda ya faru din gargadi ne da kuma kare kai daga hare-haren da HKI take kai wa a ciki kwanakin da su ka gabata.
Bugu da kari Ali Fayyadh ya yi ishara da keta tsagaita wutar yakin da ‘yan mamaya suke yi a cikin garin Khayam, ta hanyar bata hanyoyin mota da wuraren wasannin motsa jiki, tare da cewa, abinda Isra’ilan take yi baya a karkashin tsagaita wutar yaki.
Dan majalisar na kungiyar Hizbullah ya ce; Hakkin kasar Lebanon ta kare kanta, haka nan kuma hakkin al’ummar Lebanon ne su kare kansu daga wuce gona da irin HKI.
Haka nan kuma Ali Fayyadh ya yi kira ga mahukuntan kasar ta Lebanon da su bi diddigin abubuwan da suke faruwa, su kuma kasance cikin fadaka.