Kungiyar gwagwarmayar Musulunci a kasar Labanon ta Hizbullah na ci gaba da gudanar da ayyukanta na mara baya ga al’ummar Gaza, da kuma mayar da martani ga hare-haren Isra’ila kan Lebanon.
Mayakan kungiyar sun kai hari a filin jirgin saman soja na Megiddo da ke yammacin Afula da kuma sansanin Ramat David na sojojin mamaya na Isra’ila.
A ci gaba da goyon bayan al’ummar Palastinu masu tsayin daka a Zirin Gaza, da kuma kare kasar Labanon da ‘yan kasar, kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta sanar da kaddamar da hare-hare da dama kan a arewacin Falasdinu da yahudawa suka mamaye.
Harin na Hezbollah ya nufi filin jirgin saman soja na Megiddo da ke yammacin Afula har sau uku tare da harba rokoki samfurin Fadi-1 da Fadi-2.
An kuma kai wasu Hare-haren a kan sansanin sojin Isra’ila na Ramat David da filin jirgin saman soja na salvo da makami mai linzami, da kuma sansanin Amos, da ke a matsayin babbar cibiyar tallafin kayan yaki da sufuri na sojin Isra’ila a yankin arewacin kasar.
Tun da farko wakilin tashar Al Mayadeen a kudancin kasar Labanon ya rawaito cewa an harba wasu manyan rokoki guda hudu zuwa yankunan Falasdinawa da yahudawa suka mamaye.
Kafofin yada labaran Isra’ila sun bayar da rahoton cewa, hare-haren Hizbullah sun hada yankuna da dama daga ciki har da Golan, Afula, Gingar, Yafia al-Naseriyya, Migdal HaEmek, Mazraa, da yankunan al-Jalil da Haifa.