Kungiyar Hezbollah ta Lebanon ta sanar da harba gomman makaman roka zuwa arewacin Isra’ila, bayan wani hari da Isra’ila ta kai birnin Nabatieh da ke kudancin kasar inda akalla mutum 10 suka rasu.
Rundunar sojin Isra’ila ta ce akalla makaman roka 50 aka harba cikin garin Ayelet Ha-Shahar da ke arewacin kasar.
Bayanaiu sun ce mutanen da suka rasu sanadin harin ‘yan Siriya ne.
A nata banagre Syria ta yi Allah wadai da harin, tare da bayyana shi a matsayin “kisan kisa” da kuma keta dokokin kasa da kasa.
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Siriya ta bayyana a cikin wata sanarwa da ta fitar a jiya Asabar cewa, harin da Isra’ila ta kai a kudancin kasar Lebanon, wanda ya yi sanadin mutuwar ‘yan kasar akalla 10, babban cin zarafi ne ga ‘yancin kan kasar Lebanon da kuma yin barazana ga zaman lafiya da tsaro a yankin.
Ta ce ‘yan gwagwarmaya a fadin duniya suna kokarin kawo karshen ayyukan wuce gona da iri da gwamnatin Isra’ila ke yi da kuma kisan gillar da ake yi wa Falasdinawa.
Ma’aikatar ta jaddada goyon bayan Syria ga Lebanon da kuma tausayawa iyalan wadanda abin ya shafa.
Syria ta kuma kara jaddada goyon bayanta ga al’ummar Lebanon, a yayin da suke fuskantar hare-haren wuce gona da iri na Isra’ila.