Search
Close this search box.

Hezbollah, Ta Ce Sojojinta Sun Fafata Da Na Isra’ila Dake Kokarin Kutsawa

Kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ta fada yau Laraba cewa ta fafata da sojojin Isra’ila da ke kokarin kutsawa cikin kasar Lebanon, inda ta kara

Kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ta fada yau Laraba cewa ta fafata da sojojin Isra’ila da ke kokarin kutsawa cikin kasar Lebanon, inda ta kara da cewa ta kai hari kan sojojin Isra’ila a daya bangaren.

 A cikin wata sanarwa da kungiyar Hizbullah ta fitar ta ce mayakan kungiyar sun yi arangama da wasu sojojin makiya na Isra’ila da ke kokarin kutsawa kauyen Adaysseh.

Sojojin Isra’ila sun gargadi mutane da kada su yi tafiya a cikin motoci daga arewacin kogin Litani da ke kudancin Lebanon zuwa yankin kudancin kogin.

Rahotanni sun ce ana ci gaba da gwabza kazamin fada tsakanin sojojin Isra’ila da mayakan Hizbullah a kudancin kasar Lebanon, in ji rundunar sojan kasar.

A wani labarin kuma Ma’aikatar lafiya ta kasar Lebanon ta sanar cewa, an kashe mutane 55 tare da jikkata wasu 156 sakamakon hare-haren da Isra’ila ta kai cikin sa’o’i 24 da suka gabata a wasu yankuna na kasar.

Lebanon ta kuma ce mutane 1,873 ne suka mutu a kasar tun lokacin da Isra’ila da Hizbullah suka fara musayar wuta a ranar 8 ga watan Oktoban bara, ciki har da fiye da dubu tun daga ranar 23 ga watan Satumban da ya gabata.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments