Hatsarin Mota Ya Yi Sanadin Mutuwar Mutane 22 A Masar

Kifewar wata motar bas a kudancin Sinai na kasar Masar ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 22 tare jikkatan wasu 28 na daban Ma’aikatar Lafiya ta

Kifewar wata motar bas a kudancin Sinai na kasar Masar ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 22 tare jikkatan wasu 28 na daban

Ma’aikatar Lafiya ta kasar Masar ta watsa rahoton cewa: Mutane 22 sun mutu yayin da wasu 28 na daban suka jikkata, a lokacin da wata motar bas ta fasinja ta kife a Jihar Kudancin Sinai a safiyar jiya Laraba.

Ma’aikatarlafiyar ta bayyana a cikin wata sanarwa cewa: Hatsarin ya faru ne a kan wata hanya da ta haɗa biranen yawon buɗe ido na Dahab da Nuweiba a gabashin gabar tekun Sinai. An aika da motocin daukar marasa lafiya guda 20 zuwa wurin da lamarin ya faru, kuma an kai waɗanda suka samu raunuka zuwa asibiti don samun kulawa da lafiyarsu.

Ministan Lafiya na Masar Khaled Abdel Ghaffar ya bayar da umarnin “bayar da mafi girman matakin kula da lafiya ga waɗanda suka ji rauni, tare da tabbatar da samun duk kayan aiki da magunguna da ake buƙata, da kuma haɗa kai da hukumomin da suka dace a Jihar Kudancin Sinai.” Gidan talebijin na kasar Jordan ya sanar da cewa: Daga cikin waɗanda suka mutu akwai ‘yan Jordan 10 a lokacin da motar bas din fasinjar ta kife a kan hanyar Dahab-Nuweiba a Jihar Kudancin Sinai ta Masar.” Rahoton ya ƙara da cewa motar bas ɗin tana ɗauke da mutane 43, ciki har da ‘yan Jordan 22.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted