Bayanai daga Falasdinu na cewa wani hari bam da Sojojin Isra’ila suka kai a wani gida a Khan Younis, ya yi sanadin shahadar akalla mutane 23.
Sojojin Isra’ila sun kai harin ne a yankin al-Manara a kudancin Khan Younis a kudancin Gaza, inda suka kashe mutane akalla 23, kamar yadda gdian talabijin na Aljazeera ya rawaito.
Wannan dai shi ne hari na baya bayan nan mafi muni da aka kai a zirin Gaza a cikin ‘yan sa’o’i.
Tun da farko, rahotonni sun ce an samu hasarar rayuka da dama bayan da sojojin Isra’ila suka rusa wasu gine-gine fiye da 10 a Jabalia, dake arewacin Gaza, a wani hari da suka kai a Gaza.
Sojojin Isra’ila sun kuma kai harin bam a asibitin Kamal Adwan da ke arewacin Gaza, inda suka kashe kananan yara da ba a tantance adadinsu ba.
A wani labarin kuma al’amuran jin kai na ci gaba da tabarbarewa a Gaza.
Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana halin da ake ciki na jin kai a arewacin Gaza a matsayin mafi muni tun bayan barkewar rikicin.
Ya kara da cewa “Ya kamata a fara aikin rigakafin cutar shan inna amma an tilasta mana dakatar da shi saboda ci gaba da tashin hankali da rashin samun kulawa,” in ji shi.
Ma’aikatar lafiya a Gaza ta sanar a ranar Alhamis din nan cewa an samu karin mutane 42,847 da suka mutu a yankin Falasdinu tun bayan fara yaki da Isra’ila fiye da shekara guda da ta gabata.
Akalla mutane 55 ne aka kashe a cikin sa’o’i 24 da suka gabata, sai wasu dubu 100,544 da suka jikkata a zirin.