Harin Neman Shahada Ya Kashe ‘Dan Share Wuri Zauna Daya A Garin Haifa

Kafafen watsa labarun HKI sun ambaci cewa; An kai hari nau’i biyu, da ya hada amfani da motar take mutane da kuma bude wuta daga

Kafafen watsa labarun HKI sun ambaci cewa; An kai hari nau’i biyu, da ya hada amfani da motar take mutane da kuma bude wuta daga bindiga. Harin da aka kai a kusa da yankin “Yukna’am Iliyat” dake gabashin garin Haifa, ya yi sanadiyyar halakar wani dan share wuri zauna da kuma jikkata wani guda daya.

‘Yan sandan HKI sun ambaci cewa, wanda ya kai harin ya isa wurin ne a cikin motarsa, inda ya sami ‘yan share wuri zauna da yawa a tashar mota, ya kuma bude wuta akan masu wucewa da hakan ya yi sanadiyyar jikkata wasu da dama.

Ma’aikatan Agaji kuwa sun amabci cewa baya ga halaka da kuma jikkatar ‘yan share wuri zauna, an harbe mahari.

Tashar talabijin din “Cane” ta ambaci cewa; Wanda ya kai harin Bapalasdine dag acikin yakin yankin Falasdinu dake karkashin mamaya tun 1948.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments