Rahotanni daga Lebanon na cewa wani hari da sojojin Isra’ila suka kai wani gini ya yi sanadin mutuwar ‘yan jarida uku.
Tashar talabijin ta Al Mayadeen ta ce an kashe wani mai daukar hotonta a wani hari da jiragen yakin Isra’ila suka kai kan wani gidan ‘yan jarida a garin Hasbaiyya na kudancin kasar Lebanon cikin daren jiya.
An kuma bayar da rahoton kashe wasu ‘yan jarida biyu a harin da bisa ga alama an auna ma’aikatan yada labaran ne a cewar tashar.
Kisan dai na zuwa ne kwanaki biyu kacal bayan da Isra’ila ta kai wani hari ta sama kan wani ofishin kungiyar Al Mayadeen da ke da alaka da kungiyar Hizbullah da ke birnin Beirut.
An kashe ‘yan jaridar Al Mayadeen guda biyu da ke ba da rahoto kan ayyukan soji a kudancin Lebanon kan iyaka da Isra’ila a wani hari da sojojin Isra’ila suka kai a ranar 21 ga Nuwamba, 2023.