Kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ta dauki alhakin hari kan wani sansanonin sojin Isra’ila, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar soji hudu tare da jikkata wasu da dama.
Hezbollah ta fada a ranar Lahadin cewa, ta harba wani rukunin jiragai marasa matuki a sansanin horas da sojoji na Isra’ila a yankunan arewacin da ta mamaye.
Ma’aikatar lafiya ta Isra’ila ta ce akalla sojojin Isra’ila 4 ne suka mutu, yayin da wasu 61 suka samu raunuka sakamakon harin aka kai a sansanin soji na Binyamina a kudancin Haifa.
Hezbollah ta ce wannan farmakin na a matsayin martani ne ga hare-haren yahudawan sahyuniya na baya baya bab da suka hada da wanda aka kai a tsakiyar birnin Beirut inda aka kashe mutane 22 a ranar Alhamis, da kuma goyon bayan Falasdinawa a Gaza.
Kungiyar ta kuma yi barazanar kai wa Isra’ila hari, idan har ta ci gaba da kai hare-hare a kasar Lebanon.
Harin na baya-bayan nan da jirage marasa matuka na Hizbullah ya zo ne bayan da Amurka ta sanar da cewa za ta aike da tsarin kakkabo makamai masu linzami samfarin (THAAD) zuwa Isra’ila don taimakawa Isra’ila kare kanta daga hare-haren makamai masu linzami da ke shigowa.
Ministan harkokin wajen kasar Iran Seyyed Abbas Araghchi, ya gargadi kasar Amurka game da hadarin tura dakarun ta zuwa kasar Isra’ila, da nufin lura da na’urorin tsarin kakkabo makamai masu linzami ko THAAD.
Araghchi wanda ya bayyana hakan a jiya Lahadi cikin sakon da ya wallafa ta shafin yanar gizo, ya ce Amurka za ta jefa sojojin ta cikin hadari, idan har ta tura su Isra’ila domin lura da sarrafa na’urorin na THAAD kirar Amurka.