Harin Da Isra’ila Ta kai A Gabashin Kasar Labanon Yayi Sanadiyar Mutuwar Mutane 3

Rahotanni da suka fito daga kasar Labanon sun bayyana cewa jiragen sama mara matuki na HKI sun kai hari  a kudanci da gabashin kasar Labanon

Rahotanni da suka fito daga kasar Labanon sun bayyana cewa jiragen sama mara matuki na HKI sun kai hari  a kudanci da gabashin kasar Labanon kuma akalla ya kashe mutane guda 3, a ci gaba da ke ta alfarmar kasar da kuma kudurin majalisar dinkin duniya na yarjejeniyar dakatar da bude wuta da aka cimma

A jiya Alhamis isra’ila  tayi amfani da jiragen sama mara matuki wajen kai hari kan wata motar akori kura a kan hanyar dake tsakanin Majdal selm da kuma safad albatik a kudancin labanon kuma ya kashe mutum daya,

Haka  zalika sojojin lsra’ila sun hari wani dan jarida, inda suka bude wuta kan wani ma’aikacin gidan talabijin din al-mayadeen adaidai lokacin da suke aikin tattara rahoto a garin al-dhyra dake kudancin labanon,

Wadannan hare-haren wani bangare ne na salon zalunci da isra’ila ke yi  wanda keta yarjejeniyar tsagaita bude wuta ce da aka cimma a ranar 27 ga watan nuwamba na shekarar da ta gabata, da kudurin majalisar dinkin duniya mai lamba 1701 da kuma cikakken ikon mallakar yankunan labanon.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted