Shugaban kasar Iran Mahamud Pezeshkiyan ya bayyana cewa kai hare hare da makamai masu linzami, yin ruwan wuta da bama bamai ba zai taba tilastawa alummar iran mika wuya ga Amurka ba, duk da barazanar da take yi bayan ta kasa durkusar da iran ta hanyar kai hare hare da kuma killacewa.
Shugaban ya fadi hakan ne a wajen taron ranar ma’aikatan jinya ta kasa wato national Nurses day da aka gudanar a yau Alhamis ,ya kara da cewa makamai mazu linzamu ba za su tsorata alummar iran ta mika wuya ba, amma idan kan mu ya rabu to makiya za su iya cimma burinsu
Hakalika pezeshekiyan yayi gargadi game da makircin da makiya ke kullawa na haifar da rarrabuwar kai a cikin gida da haifar da matsaloli don karya karfin alumma da hadin kai da take da shi, kuma ya jaddada cewa alummar iran sun sha alwashin tsayawa kyam don fuskantar makircin makiya da kuma matsin lamba da suke kara yi kan alummar iran,
Daga karshe yayi kira ga jama’ain gwamnatin da su guji furta duk wasu kalamai ko aikata wani aiki da zai sanya alamar tambaya ga hadin kan kasar, kuma ya bukaci da su yi amfani da dukkan albarkatun da ake da shi wajen karfafa amincewar alumma.