Yahudawan sahyoniyya wadanda suke kaiwa Falasdinawa hare hare a yankin yamma da kogin Jordan sun kara yawan hare harensu da kasha 63% a rabin farko na wannan shekara ta 2026.
Kamfanin dillancin labaran KAN ya bayyana haka a jiya Litinin ya kuma kara da cewa, ya sami wannan labarin ne da cibiyoyin tsaro na HKI kanta. Cibiyar ta kara da cewa wadan nan hare hare a wajen wasu kungiyoyin kasa da kasa ayyukan ta’addancin ne.
Labarin ya kara da cewa yahudawan sun kai hare hare kan Falasdinawa a yankin yamma da kogiun Jordan har sau 660 a rabin farko na wannan shekara kadai, kuma yafi na shekara ta 2025 wanda ya kasance 405.
Har’ila yau labarin ya kara da cewa hare hare wadanda Falasdinawa suke kaiwa ‘Jami’an tsaron’ yahudawan ya karu da kasha 50% wanda yawansu ya kai 45 a rabin wannan shekarar.
Hakama yawan falasdinwa da suka jikata sanadiyyar wadan nan hare hare ya kai ga shahadar mutane 6 da kuma jikatar wasu 140. Kafin haka a shekarar da ta gabata falasdinawa 82 ne suka ji rauni.