Hare-haren Isra’ila Sun Kashe Falasdinawa 26, A Nuseirat

Rahotanni daga Falasdinu na cewa hare-haren da Isra’ila ta kai kan wani gida da ke sansanin ‘yan gudun hijira na Nuseirat ya yi sanadiyar mutuwar

Rahotanni daga Falasdinu na cewa hare-haren da Isra’ila ta kai kan wani gida da ke sansanin ‘yan gudun hijira na Nuseirat ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama da suka hada da yara da mata, a cewar likitoci.

A yammacin ranar Juma’a, sojojin gwamnatin kasar sun kai hari ta sama kan wani gini a sansanin da ke tsakiyar zirin Gaza.

Likitoci sun ce an kashe akalla mutane 26, daga cikinsu akwai yara 6 da mata biyar sai kuma akalla mutane 60 da suka jikkata.

Kakakin hukumar tsaron farar hula Mahmoud Basal ya kuma ce harin “ya lalata gidaje da dama da ke makwabtaka da su.”

A wani lamari na daban kuma, wata yarinya ta mutu lokacin da wasu makaman roka na Isra’ila suka abkawa wasu tantunan ‘yan  gudun hijira a kusa da yammacin sansanin.

Ma’aikatar lafiya a Gaza ta sanar a yau Asabar cewa adadin wadanda suka mutu ya zarce 44,660, a cikin kusan watanni 14 na yakin kisan kare dangi da Isra’ila ta yi kan zirin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments