Sojojin mamayar Isra’ila sun yi furuci da cewa: Kwamandan sojinsu na bataliyar Manshiya da ke arewacin gabar kogin Jordan ya samu rauni
Majiyar rundunar sojojin mamayar Isra’ila ta tabbatar da cewa: Kwamandan bataliyar Manshiya da ke kula da shiyar arewacin gabara kogin Jordan ya samu rauni sakamakon fashewar wata nakiya a kan hanyar shigewarsu a lokacin da suke Shirin kai hari kan garin Tulkaram na Falasdinu.
A sanarwar da rundunar sojin ta fitar ta ce: Nakiyar da aka binne a karkashin kasa ta tarwatse ne a daidai lokacin da mota mai sulke da take dauke da kwamandan rundunar da take kula da gabar yammacin kogin Jordan Birgediya Janar Yakiy Dolf da kwamandan bataliyar yankin Manshiya, Kanar Ayoub Kayouf.
Sannan sojojin mamayar ta Isra’ila sun kaddamar da farmaki kan birnin Tulkarm da sansaninsa tun da wayewar garin jiya Talata.
A gefe guda kuma, ma’aikatar lafiya ta Falasdinu ta sanar da shahadan Falasdinawa 5 tare da jikkata wasu na daban a hare-haren da jiragen saman yakin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai kan sansanin Tulkaram.