A daidai lokacin da ake batun shiga mataki na biyu a yarjejeniyar tsagaita wutar yaki, sojojin Haramtacciyar Kasar Isra’ila sun ce, ba za su janye ba daga wuraren da su ka shiga ba a cikin zirin Gaza.
Kamfanin dillancin labarun “Irna” ya nakalto cewa a daidai lokacin da ake Shirin shiga mataki na gaba a karkashin tsagaita wutar yakin Gaza, manzon musamman na Amurka a gabas ta tsakiya Stev Witkoff ya sanar da cewa sojojin Isra’ila ba za su fice daga wuraren da suke ciki ba a Gaza.
Batun ficewar sojojin Isra’ila daga yankunan da su ka shiga a Gaza yana karkashin yarjejeniyar tsagaita wutar yakin wacce shugaban kasar Amurka Donald Trump sanar da ita.
Karya yarjejeniyar tsagaita wuta dai ba bakon abu ne a wurin sojojin Haramtacciyar Kasar Isra’ila. Kusan babu wata rana ta Allah da sojojin mamayar ba su kai hari akan yankin na Gaza.
A can Tel Aviv, fira ministan haramtacciyar Kasar Isra’ila ya sanar da cewa, sun karbi gawa ta karshe ta fursunonin yaki daga yankin Gaza,yana mai kara da cewa, abinda yake a gabansu shine batun kafa gwamanti ta kwararru a yankin na Gaza.
Majiyar Falasdinawa kuwa ta ambata cewa matukar ‘yan sahayoniyar ba su janye ba,to zai kawo cikas wajen fara aiki da zagaye na biyu na Shirin tsagaita wutar.
A gefe daya,Falasdianwa 15 sun yi shahada sanadiyyar hare-haren da sojojin mamaya su ka kai a gabashin Gaza ta hanyar amfani da jiragen sama na yaki da kuma manyan bindigogi.
Al’ummar Falasdinu dai suna rayuwa a cikin matsananciyar wahala saboda saukar ruwan sama da kankara a wasu yankunan da hakan ya lalata hemomin da ‘yan hijira suke rayuwa a ciki.