Har Yanzu Ba’a Tantance Tasirin Yakin Amurka Kan Iran Ba

har yanzu baa tantance tasirin da yakin amurka ta yi da iran yayi ba, a kasuwannin duniya

Ministan tattalin arziki na kasar Rasha y ace tsarin kasuwanci na kasa da kasa zai fuskanci tasirin da yakin da Amurka ta kaddamar kan kasar iran yayi, a kasuwannin  duniya na tsawon lokaci , kuma har yanzu kwararru basu tantance irin mummunar asarar da hakan ya jawo  ba,

Maxim Reshtnikov ya bayyanawa kamfanin dillanci labarai na Taas cewa bayan taron kungiyar kasashen G20 a milweukee ya nuna cewa hare hare da aka kai a yammacin asiya shi ne babban dalilin da ya kawo cikas a kasuwannin duniya,

Yace a fili yake kasuwanci na duniya zai fuskanci sakamako na dogon lokaci wanda har yanzu kwararru basu tantance cikakken girman yawan asarar da yakin ya jawo ba, sai dai bangaren illar da yakin na kasashen tekun fasha ya jawo ya riga ya bayyana a tsarin kasuwanci a zangon farko na wannan shekarar

kwararru a hukumar kasuwanci ta duniya sun lissafa cewa tarnaki da aka samu ga jiragen ruwa a mashigar Hurmuz ya yanke yawan kayan da ake fitarwa da kashi 9.7 cikin dari na kayan da ya kamata a shigo da su da kashi 12 a wancan lokacin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted