Fadada Sabbin Gine- ginen Isra’ila Wata Sabuwar Mamaye Ce

kungiyar Hamas ta nuna cewa irin fadada sabbin gine gine da isra'ila ke yi yana nuna aniyar ta na sake mamaye falasdinu

Kungiyar gwagwarmaya ta Hamas tayi tir da amincewar da isra’ila tayi da dokoki 18 da ake yi wa gyaran fuska kan batun yankunan da zaa gina sabbin matsugunan yahudawa yan share wuri zauna, a inda ta mamaye a gabar yammacin kogin jodan, ta ce wannan matakin yana nuna bakar aniyarta ta sake mamaye wasu yankunan falasdinawa da kuma kara fadada ikonta a yankin

Haka zalika kungiyar ta jaddada cewa tsarin isra’ila na gina sabbin matsugunnai ba zai bawa gwamnatin tel aviv hakki ko yanci kan filayen falasdinawa ba , kuma ba zasu iya tabbatar da zaman lafiya ko tsaro a yankunan ba,

Kungiyar Hamas ta yi kira ga majalisar dinkin duniya da ta yi aiki da nauyin da ya ratawa a wuyanta, mai makon ta takaita ga mayar da martani wajen yin tir da fadada gine -gine da Isra’ilan ke yi ,kuma ta yi kira ga manyan kasashen duniya su dakatar da isra’ila daga daukar wannan mataki, kuma su tilasta mata biyayya ga dokokin kasa da kasa da kuma kudurorin majalisar dinkin duniya.

Wannan yana zuwa ne duk da matsin lamba da fira ministan isra’ila Benjamin Natenyaho yake fuskanta na kasa da kasa, amma ya ci gaba da aiwatar da gine-gine da kuma fadada samar da matsunnai a fadin gabar yammacin kogin Jodan,kuma ya sha alwashin yin tasiri ga sauran yan gudun hijira da su mamaye yankunan falasdinawa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted