Hamas : tattaunawa ce kawai mafita ta sakin wadanda ake garkuwa dasu

Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi imanin cewa barazanar da Isra’ila ke yi na sake dawo da yaki a zirin Gaza ba ta da

Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi imanin cewa barazanar da Isra’ila ke yi na sake dawo da yaki a zirin Gaza ba ta da amfani, tana mai cewa tattaunawar tsagaita bude wuta ce hanya daya tilo da Isra’ila za ta iya ceto rayukan ‘yan kasarta da take garkuwa

ranar Litinin 10 ga watan Maris, kungiyar ta ce Firaministan Isra’ila Benyamin Netanyahu na kawo cikas ga aiwatar da yarjejeniyar saboda wasu dalilai na rajin kansa da kuma na siyasa kawai.

Hamas ta kuma kara jaddada aniyar ta na aiwatar da yarjejeniyar, inda ta bayyana aniyar ta na kaddamar da shirin tsagaita wuta a mataki na biyu ba tare da bata lokaci ba.

Har ila yau kungiyar ta ce gwamnatin Isra’ila tana ci gaba da karya yarjejeniyar tare da kin shiga mataki na biyu, tana mai cewa wannan “jinkirin” ya kara mayar da ita saniyar ware a duniya.

Hamas ta jaddada cewa, masu shiga tsakani na kasa da kasa ne suka yi shawarwari da ita, kuma kasashen duniya sun amince da ita, don haka ta jaddada bukatar tabbatar da aiwatar da ita yadda ya kamata daga gwamnatin kasar don tabbatar da sako mutanen da ta kama.

Tun da farko kakakin kungiyar Hamas Abdul Latif al-Qanou ya bayyana sassaucin da kungiyar ta nuna a lokacin tattaunawar baya-bayan nan da masu shiga tsakani na Masar da Qatar, da kuma wakilin shugaban Amurka Donald Trump a birnin Doha, ya kuma jaddada fatansu na cimma nasarar kammala wannan shawarwarin da Isra’ila.

Ya kara da cewa tattaunawar ta Doha ta shafi kawo karshen yakin, janyewar Isra’ila da sake gina yankin Zirin Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments