Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi Allah wadai da mummunan hare-haren da Isra’ila ta kai kan wasu gine-gine biyu a arewacin Gaza wanda ya kashe akalla mutane 75.
A wata sanarwa da kungiyar Hamas ta fitar ta ce akasarin wadanda harin na Beit Lahia ya shafa mata ne da kananan yara.
Kungiyar ta ce tawagogin likitocin sun kasa isa yankin da abin ya shafa yayin da Isra’ila ke ci gaba da hana su shiga arewacin Zirin da aka yi wa luguden wuta.
Tun kwanaki 50 da suka gabata Isra’ila ta killace yankin a wani kazamin harin bama-bamai a kan gine-ginen fararen hula.
Kungiyar ta ce gwamnatin Isra’ila tana kai hari kan fararen hula da ba su da kariya, musamman asibitoci, tare da kashe likitoci, ma’aikatan jinya da kuma jami’an tsaron fararen hula, tare da hana samun damar kai wadanda suka jikkata domin yi musu magani.