Hamas ta yi Allah wadai da Isra’ila kan keta yarjejeniyar tsagaita bude wuta

Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi Allah wadai da Isra’ila kan keta yarjejeniyar tsagaita bude wuta, tare da yin Allah wadai da ci gaba

Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi Allah wadai da Isra’ila kan keta yarjejeniyar tsagaita bude wuta, tare da yin Allah wadai da ci gaba da rufe mashigar Rafah a matsayin wani mataki na karan tsaye ga sulhun.

A cikin wata sanarwa da ta fitar, Hamas ta yi Allah wadai da matakin da firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya dauka na jinkirta bude mashigar Rafah  tare da bayyana hakan a matsayin karya sharuddan tsagaita bude wuta da kuma kaucewa alkawurran da aka dauka ga masu shiga tsakani da masu bada garantin.

Kungiyar ta yi gargadin cewa rufewar yana kuma kawo cikas ga zuwan tawagogi na musamman domin zakulo gawarwakin da ke karkashin baraguzan gine gine da kuma gano wadanda suka mutu, ciki har da gawarwakin mutanen Isra’ila da aka yi garkuwa da su da za a mayar da su karkashin yarjejeniyar tsagaita bude wuta. Kungiyar masu fafutukar kare hakkin bil adama ta ce Isra’ila ta keta yarjejeniyar tsagaita bude wuta sau 47 tun bayan aiwatar da ita a makon jiya, inda ta kashe Falasdinawa 38 tare da jikkata wasu 143 na daban

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments