Kungiyar Hamas ta zargi Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu da gaza cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza, biyo bayan tattaunawar kwanaki biyu da aka yi a birnin Doha da aka kammala ranar Juma’a, wacce kungiyar ba ta shiga cikinta ba.
Kungiyar ta mayar da martani a hukumance a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi bayan nazarin sakamakon shawarwarin da kasashen Qatar da Masar da kuma Amurka suka gabatar.
Hamas ta yi kira ga masu shiga tsakanin da su gabatar da wani sahihin shiri don aiwatar da shawarwarin da aka amince da su a ranar 2 ga watan Yuli.
A cikin sanarwar Hamas ta zargi Netanyahu da ci gaba da kawo cikas a hanyar cimma yarjejeniya.”
Kungiyar ta jaddada cewa sabuwar shawara da aka gabatar yayin tattaunawar ta yi dai-dai da sharuddan Netanyahu, wadanda suka hada da kin amincewa da tsagaita bude wuta na dindindin da duk wani janyewar sojojin Isra’ila daga Gaza.
Kungiyar gwagwarmayar ta yi nuni da cewa, shawarar ta kuma nuna dagewar Netanyahu na ci gaba da rike iko a yankunan Gaza da suka hada da mahadar Netzarim, mashigar Rafah, da kuma hanyar Philadelphi.
Bugu da kari, Hamas ta soki sabbin sharuddan da Netanyahu ya gindaya kan tattaunawar musayar fursunoni.
A don haka a cewar Netanyahu ne ke da alhakin dakile kokarin masu shiga tsakani na cimma yarjejeniya,” in ji ta.