Hamas Ta Sanar Da Shahadar Wani Jagoranta Da HKI Ta Kashe A Lebanon

Dakarun “Kassam” na kungiyar Hamas sun sanar da shahadar Muhammad Shahin wanda daya ne daga cikin kwamandojinta da ya yi shahada sanadiyyar harin da HKI

Dakarun “Kassam” na kungiyar Hamas sun sanar da shahadar Muhammad Shahin wanda daya ne daga cikin kwamandojinta da ya yi shahada sanadiyyar harin da HKI ta kai masa a birnin Saida na kasar Lebanon.

Sanarwar ta dakarun “Kassam” ta ce, Muhammad Ibrahim Shahin wanda ake yi wa lakabi da Abul-Bara’a ya yi shahada ne a karkashin “Tufan-ak-Aksa” bayan da ‘yan mamayar HKI su ka yi masa kisan gilla a garin Saida dake kudancin Lebanon a jiya Litinin.

Har ila yau dakarun Kassam sun yi bayani akan rawar da shahidin ya taka a fagen gwgawarmaya da jihadi akan ‘yan mamaya, tun daga boren Intifada na Aksa, har zuwa farmakin guguwar Aksa.

Haka nan kuma bayanin na Kassam ya ce, Abul-Baraa ya riski dan’uwansa Shahin Hamzah Shahid wanda ya gabace shi da yin shahada da kuma sauran ‘yan’uwansa shahidai masu tsarki.

Kassam din ta yi alkawalin ci gaba da tafiya akan tafarkin shahidin na jihadi da gwagwarmaya har zuwa cimma manufofin al’ummar Falasdinu na ‘yanto da Falasdinu da fursunonin da suke kurkuku da kuma komawar  Falasdinawa ‘yan hijira zuwa gida.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments