Hamas Ta Harba  Wa HKI Makamai Masu Linzami 20 A Cikin Kwanaki 9

Radiyon sojan HKI ya bayar da labarin cewa, a  cikin kwanaki 9 na bayan nan kungiyar Hamas ta harba makamai masu linzami 20 daga cikinsu

Radiyon sojan HKI ya bayar da labarin cewa, a  cikin kwanaki 9 na bayan nan kungiyar Hamas ta harba makamai masu linzami 20 daga cikinsu da akwai 14 da su ka tashi daga Arewacin Gaza.

Radiyon sojan HKI ya kuma ce,jiniyar gargadi ta rika tashi a cikin sansanonin ‘yan share wuri zauna na; Nativ” da Ha’asara” da suke a kusa ga yankin zirin Gaza.

Kungiyar gwagwarmayar ta Falasdinawa tana harba wadannan makaman masu linzamin ne daga yankunan da sojojin HKI su ka  dauki shekara daya suna nike su, da kuma lalata duk wani abu mai afmani a cikinsu, musamman arewacin zirin Gaza.

A cikin watan Disamba na shekarar da ta shude ma dai mai Magana da yawun sojojin mamaya ya ce, na’urorinsu sun kakkabo makamai masu linzami 5 da aka harbawa sansanin ‘yan share wuri zauna na garin Sidrot da kuma “Nir-Am.

Tashar talbijin ta 13; ta ce makami mai linzamin da aka harba wa matsugunin ‘yan share wuri zauna na “Kibots-Nir-Am” ya haddasa barna.

Ita kuwa jaridar “Yadiot-Ahranot” ta bayyana cigaba da harba makamai masu linzamin da Falasdinawa suke yi daga Gaza da cewa, yana da daure kai.

Dama dai tun da fari, wani tsohon ministan HKI Haim Ramon ya ce; Babu wata nasara da sojojinsu su ka samu a Gaza, domin har yanzu ba su murkushe Hamas ba, ba su kuma iya kawo karshen mulkinta a Gaza ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments