Wani babban jami’in kungiyar Hamas a Gaza ya bada sanarwan cewa, kungiyarsa ta gabatar da sunayen mutane fiye da 40 wadanda yan kasa ne kuma kwarraru, don sanyasu a mukaman harkokin gudanarwan zirin gaza.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Muhammad Nazal, wani babban jami’I na kungiyar yana fadawa tashar talabijin ta Aljazeerah na kasar kasar Qatar haka, a wata hirar da ta hada su a jiya Asabar.
Nazal ya kara da cewa, wadannan masana kuma kwararru a harkokin gudanarwa za su taimaka wajen ganin an gabatarwa mutanen Gaza ayyukan jinkai don fidda Falasdinawa a Gaza daga mummunan halin da suke ciki a bangarori daban daban na rayuwa.
Kimanin wata guda da ya gabata ne kungiyar ta bada sanarwan cewa zata mika harkokin gudnarwa na zirin gaza ga wasu falasdinawa kwararru wadanda zasu gudanar da harkokin a gaza, bisa shawarar da shugaba Trump ya bayar danagne da tsagaita wuta.